This translation is incomplete. Please help translate this article from English.

Wannan bayani ya fayyace wasu ƙa’idoji da sai an cikasu kafin a sami rarraba aikace-aikace ta hanyar Firefox Marketplace. Waɗannan ƙa’idoji an shiryasu ta yadda za su dace da bukatun mai samarwa da kuma mai amfani da aikace-aikace daga Firefox Marketplace. Masu samarwa na bukatar tsari mai sassauci, mai ɗorewa, marar tsauri wanda za su iya amincewa da shi domin ci gaban kasuwancin. A ɗaya ɓangaren kuma, masu amfani su na bukatar tabbatarwa cewa aikace-aikacen ba su da haɗari, za su yi aiki a na’urarsu, kuma aikace-aikacen za su yi abin da aka ce za su yi. Ƙa’idojin da aka shimfiɗa a ƙasa an shiryasu ne domin tabbatar da daidaito tsakanin waɗannan bukatu.

Waɗannan su ne abubuwan da Mozilla ke tsammani me nazarin aikace-aikace ya ƙunsa ko bai ƙunsa ba:

 • Za’a gudanar da ƙa’ida cikin adalci, tausayawa, da kuma ɗorewa. Ka da a shirya gudanar da nazarin aikace-aikace da niyyar kaka-gida, sai dai a matsyin wata mahaɗa ta tuntuɓa domin taimakawa masu samarwa su sami ƙarin nasara.
 • Masu nazari ba ƙungiyar masu tambayoyi ba ne! Lokacin gudanar da nazari, mutum zai duba manufar aikace-aikacen sannan ya ɗauki wasu mintina ya na gwada aikace-aikacen tamkar dai yadda mai amfani da shi zai yi.
 • Idan wani daga cikin aikace-aikacen ya ƙi aiki, za’a baiwa mai samarwa cikakken bayanin matsalar da aka samu, matakai na sake samarwa, da kuma in zai yiwu, mai nazari ya yiwa mai samarwa jagoranci ta hanyar ba shi bayani na dandalin yanar gizo wanda ya dace domin samun bayanan da suka dace, ko bayar da shawarwari game da gyaran da ya kamata a yi.
 •  Masu nazari ba sa yanke hukunci na yadda ya kamata aikace-aikace suzama,sai dai kawai yadda ya kamata su yiaiki.Misali, aikace-aikacen da yake da jan rubutu a kan takarda mai ruwan-goro ba za’a ƙi amincewa da shi sabo da ba shi da kyau ba, sai dai idan an kasa karanta shi.
 • Ko yaushe muna bawa masu samarwa dama. Idan ba’a tabbatar ko za’a ƙi amincewa da aikace-aikace ba, masu nazari su fara yin tambayoyikafin su nuna rashin amincewa. Ba za’a ƙi amincewa da aikace-aikace ba (da gan-gan) sabo da matsaloli na manufa waɗanda sun fi ƙarfin mai samarwa ya sarrafasu; to amma za mu iya jinkirta amincewa idan muka kasa saka aikace-aikace su yi aiki.

Tsaro

Za’a sami cikakkiyar taswirar bayanin tsaro na aikace-aikace a nan: https://wiki.mozilla.org/Apps/Security

 • Dole a samar da manufar aikace-aikace daga tushe guda kamar na aikace-aikace.
 • Dole a samar da manufar aikace-aikace mai ɗauke da saɗarar application/x-web-app-manifest+json.
 • Aikace-aikace kada su ƙunshi redirects ko iframes domin loda abinda ke ciki wanda mai samarwa bai yi izinin amfani da shi ba.
 • Dole a ambaci takamaiman abinda ake neman izini a manufar aikace-aikacen tare da fayyace dalilin neman izinin.
 • Aikace-aikace na type zai gudanar da ƙarin bincike, wanda ya haɗa da nazarin lamba, domin kaucewa faɗawa tarkon ‘yan-damfara da kuma gudun rasa bayanai na mai amfani wanda ya ke da damar APIs.
 • Bayanan-Manufofin-Tsaro (CSP) da aka yi bayani a manufofin aikace-aikace su ne ke tantance me aikace-aikacen za su iya yi. Shiryayye, idan ba’a yi bayani ba, domin aikace-aikace marasa damammaki, dai dai su ke tamkar ko wace irin tashar yanar gizo; aikace-aikacen type mai samun dama na da ƙarin restrictive default.  Ingantaccen rahoto wanda aka samar lokacin aikawa zuwa Firefox Marketplace zai nuna cewa an sami saɓa CPS na nan gaba a aikace-aikacenka – amma ka kiyaye wasu gudanarwa da ayyuka na ɗakunan karatu waɗanda ba za ka yi amfani da su ba.

Na ƙashin-kai

 • Dole mai samarwa ya haɗa da manufofi na ƙashin-kai lokacin miƙawa, har da wasu tsare-tsare da ake bukata na shiryawa ko abinda wannan manufa ta ƙashin-kai za ta ƙunsa. Saki jikinka ka yi amfani da privacy policy template. Kuma za ka iya duba privacy policy guidelines.

Abinda ke ciki

 • Duk wasu aikace-aikace da suka saɓa da Bayananmu na Abinda ke Ciki waɗanda aka ambata a ƙasa ba’a yarda da su ba. Idan kana zaton kana da wani ƙorafi, tambayi ƙungiyar masu nazari tamu domin bayani, ko da ba’a shirya miƙa aikace-aikacen ba tukuna. Muna so mu taimakeka ka tsaya a kan abinda ya ke shi ne dai dai, maimakon ɓata lokaci wajen abinda za’a ƙi amincewa da shi.
 • Farawa daga cikin watan Janairu 2014, dole duk aikace-aikace su sami matsayi daga Gamayyar Tantance Shekaru ta Duniya (IARC).  Domin samun nuna wannan matsayi, zamu baka wata takardar tambayoyi lokacin da kake ƙoƙarin aikawa, kuma za ka sami yadda za ka tantance matsayin nan take. Akwai bayanin yadda za ka tantance matsayin a here.
 • Hotunan shafin kwamfuta da kwatance da aka aikawa Firefox Marketplace dole su yi dai dai da aikace-aikacen. Kana iya haɗawa da hotuna 1-2 na "kasuwanci" waɗanda su ka nuna dacewa, kwatanta kamanni, ko kuma masu bayar da sha’awa, to amma lallai a sami hoton shafin kwamfuta na aikace-aikacen a lokacin da ya ke aiki a ƙalla guda ɗaya, ta yadda masu amfani za su ga misali na abinda za su samu a haƙiƙa. Idan hoton shafin kwamfutar ya sami ɗige-ɗige ko kuma hoton allon fuskar kwamfuta ne, to lallai ne ka haɗa da hoton shafin kwamfuta na gudanarwar aikace-aikacen.
 • A manufar aikace-aikace, locale keys dole su dace da fassarar sunan da aka ba shi wanda yake da tallafin aikace-aikacenka. Idan ka bayar da suna a yaren Polish, masu amfani na tsammanin samun wannan aikace-aikace a wannan yaren.
 • Alamar aikace-aikacen dole ta dace da tsarin Firefox OS app icons style guide. Girman alama ta 128 x 128 kawai ake bukata, amma muna bayar da shawara cewa alamar na iya kaiwa 512 x 512 (domin ƙarin bayani, duba Icon implementation for apps.) Ka lura da cewa alamar na iya zama da’ira, mai kusurwa huɗu, ya danganta da tsarin da aka bayar.

Jagoran abin da ke ciki

Wannan jerin ya kwatanta yanayin abin da ke ciki waɗanda ba su dace da Firefox Marketplace ba. An bayar da wannan jeri ne a matsayin misali, ba tabbatacce ba, kuma za’a iya sabunta shi. Idan an sami wani aikace-aikace da ya saɓa da bayanan jagoran abin da ke ciki, Mozilla na da dama ta cire aikace-aikacen cikin gaggawa daga Firefox Marketplace.

 • Babu kayayyakin hotunan batsa, ko kuma wani nuni ga jima’i ko tashin hankali.
 • Babu abin ciki da ya take haƙƙin wani, wanda ya haɗa da kayan nazarce-nazarce ko kayan da suka haɗa da haƙƙi ko haƙƙoƙin na wani mutum ko wasu mutane.
 • Babu abin ciki da za’a tsara wanda zai cutar da Mozilla ko masu amfani (kamar lamba ta sharri, virus, kayan leƙen asiri ko kayan cutarwa).
 • Babu abin ciki haramtacce ko wanda zai tallafawa haramtattun ayyuka.
 • Babu abin ciki da aka yi domin ha’inci, yaudara, damfara ko aka shirya domin satar bayanai ko yin sauran abubuwa na satar bayanan jama’a.
 • Babu abin ciki da zai taimakawa caca.
 • Babu abin ciki da za’a yi amfani da shi domin tallata haramtattu ko ayyukan da suke da tsari.
 • Babu abin ciki da zai tauye yara.
 • Babu abin ciki da ya ƙasƙanta, kawo barazana, rura rikici a kan, ko kuma ƙarfafa ayyukan ƙyama a kan wani mutum ko wata ƙungiya a kan banbancin shekaru, jinsi, ƙabila, harshe, asalin ƙasa, addini, mu’amalar jinsina, naƙasa, addini, wurin zama ko wani kason da aka bawa tsaro ko tsangwamar Magana.
 • Babu abin ciki da zai karkatar da mai amfani domin yanke hukunci wajen yin siyayya.

Aiki

 • Mai nazari dole ya iya gudanar da ayyukan farko na siffar aikace-aikacen da aka tallata. Za’a bayar da rahoto na rashin ƙayatarwa da ƙananan matsaloli zuwa ga mai samarwa, amma wannan ba zai hana a amince da aikace-aikacen ba.
 • Aikace-aikacen ba za su miƙa kai ga aikin na’ura ba ko daidaituwa.

Amfani

 • Mai samarwa dole ya yi ƙoƙari wajen inganta tsarin aikace-aikacen domin waɗanda aka nufa a fagen. Manufar wannan bukatar ita ce domin zaƙulo gazawa, misali:
  • Aikace-aikacen da aka aika domin wayar hannu wanda a haƙiƙa dandalin yanar gizon na kwamfuta ne.
  • Aikace-aikacen da a haƙiƙa ba zai iya mamaye sararin da ake da shi na fuskar kwamfuta ba (yi tunanin aikace-aikace mai 320x480 wanda kawai ya iya zama a kusurwar saman allon kwamfuta, yayin da sauran wurin ya zama babu komai. Wannan haƙiƙa ba haka aka nufa ba!)
 • Dole aikace-aikacen ya yi amfani da hanyarsa ta gewayawa kuma kada ya dogara da mai gewayawa na chrome ko kuma a kan allon madannin kwamfuta mai komawa baya, wanda ba a duk na’ura ake samunsa ba.
  • Misali, za’a ƙi amincewa da aikace-aikace idan mai nazari ya gewaya a cikin aikace-aikacen amma ya kasa dowawa baya. Aikace-aikace BA’A bukatar su yi amfani da madannai waɗanda su ke game-gari a aikace-aikacen da aka saba da su.
  • A kan Firefox OS v1.1 ko sama da haka, ka na iya ƙara manufar chrome sosai domin samun cikakken daɗi na madannan gewayawa.
 • Abubuwan gewayawa, misalin madannai da mahaɗi, dole su zama masu sauƙi wajen dannawa ko taɓawa.

Manufar jerin da aka datse

Ba ma fatan amfani da ita, to amma muna da dama mu cire ("datse jeri") na duk wasu aikace-aikace waɗanda daga bisani aka gano sun saɓawa ɗaya daga cikin sharuɗɗanmu na tsaro, na ƙashin-kai, ko abubuwan da ke ciki, ko aikace-aikacen da suka ƙasƙantar da ayyukan kwamfuta ko haɗin yanar gizo. Sanar da masu samarwa bisa matsayin da ake ciki kafin a datse aikace-aikace, za’a ɗaukeshi a matsayin kishi har sai mun sami wani bayani saɓanin hakan, kuma zai sami cikakken tallafi daga ƙungiyar masu nazarin aikace-aikace domin sanar da abinda ke faruwa kuma a magance matsalar. Kaɗan daga cikin misalai na yanayin da zai jawo a datse jeri sun haɗa da:

 • Leƙen asiri
 • Damfara
 • Canja abin da ke ciki daga Hotunan Wasan Yara v1.0 zuwa na Tashin Hankali v1.0 (ba tare da sabunta matsayin abin da ke ciki ba)
 • Rashin kyawun mu’amala na aikace-aikace ga kaso mafi yawa na masu amfani – ƙasƙantar da yadda wayar hannu ke aiki, jawo sake kunnawa, jawo asarar bayanai na mai amfani, da sauransu inda masu amfani ba za su iya faɗar cewa sabo da aikace-aikacen ba ne kuma aka kasa warwarewa ta hanyar sake kunna na’urar.
 • Aka yi amfani da aikace-aikacen domin kai hari a kan haɗin yanar gizo, kamar musanta rarraba aikace-aikace (DDOS).

Ƙarin bayani

Waɗannan hanyoyi za su ƙara bayani a kan yadda za’a gudanar da nazari da kuma masu nazarin aikace-aikace:

 • Reveiwers test criteria — wannan shafin ya bayyana irin gwajin da mai nazarin aikace-aikace zai gudanar a kan aikace-aikacenku
 • App reviewers — yadda za ka tuntuɓi ƙungiyar masu nazarin aikace-aikace kuma ka shiga zuwa nazarin aikace-aikace

Document Tags and Contributors

Contributors to this page: DevonB
Last updated by: DevonB,